Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rimmon

8 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da suka juya suka juya suka tsere zuwa wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, Isra’ilawa suka kashe mutum dubu biyar a kan hanyoyi. Suka yi ta matsa wa mutanen Benyamin har zuwa Gidom suka kashe mutum dubu biyu kuma.

  2. Amma mutane ɗari shida suka juya suka tsere wajajen hamada zuwa dutsen Rimmon, inda suka zauna wata huɗu.

  3. Sa’an nan dukan taro suka aika wa mutanen Benyamin da suke a Dutsen Rimmon cewa yaƙi ya ƙare, yanzu sai salama.

  4. To, ɗan Shawulu yana da ’ya’ya maza biyu da suke shugabannin ’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su ’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin,

  5. To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.

  6. Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,

  7. Amma ina fata Ubangiji zai gafarta wa bawanka saboda abu guda. Bari yă gafarta mini sa’ad da na raka sarkina zuwa haikalin Rimmon domin yă yi sujada, bari Ubangiji yă yi wa bawanka gafara saboda wannan.”

  8. Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;