Skip to content

Rechab

4 ayoyi · 2 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Rechab

  1. To, ɗan Shawulu yana da ’ya’ya maza biyu da suke shugabannin ’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su ’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin,

  2. To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.

  3. Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.

  4. Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,