Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Punishment: Delayed punishment

16 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Delayed punishment

  1. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.

  2. Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, Sela mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.

  3. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  4. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  5. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  6. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  7. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  8. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  9. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  10. za su sami sakayyar abubuwan da suka yi su kuma ƙoshi da sakayyar makircinsu.

  11. In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba.

  12. Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah.

  13. Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.

  14. Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba.

  15. Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya? Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba? Hallaka da tashin hankali suna a gabana; ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.

  16. Saboda haka ba a bin doka, shari’a kuma ba ta aiki. Mugaye sun kewaye masu adalci don a hana gaskiya tă yi aiki.