Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Phylactery

10 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Wannan abin tunawa zai zama muku alama a hannunku, da kuma a goshinku cewa dokar Ubangiji tana a bakinku. Gama Ubangiji ya fitar da ku daga Masar da hannu mai iko.

  2. Za tă kuma zama alama a hannunku da kuma shaida a goshinku cewa Ubangiji ya fito da mu daga Masar da hannunsa mai iko.”

  3. Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

  4. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.

  5. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.

  6. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

  7. Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku.

  8. Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.

  9. Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.

  10. “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsufantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;