Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pelethites: A part of David's bodyguard

5 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da A part of David's bodyguard

  1. Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.

  2. Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.

  3. Yowab ne yake shugabancin dukan rundunoni; Benahiya ɗan Yehohiyada ne yake shugabancin Keretawa da Feletiyawa;

  4. Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon.

  5. Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.