Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pelethites

6 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Benahiya ɗan Yehohiyada ne shugaban Keretawa da Feletiyawa, wato, sojoji masu gadin Dawuda, sa’an nan ’ya’yan Dawuda maza su ne mashawartan sarki.

  2. Dukan mutanensa suka wuce gabansa, tare da dukan Keretawa da Feletiyawa; da dukan mutane ɗari shida na Gittiyawan da suka raka shi daga Gat, suka wuce gaban sarki.

  3. Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.

  4. Yowab ne yake shugabancin dukan rundunoni; Benahiya ɗan Yehohiyada ne yake shugabancin Keretawa da Feletiyawa;

  5. Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon.

  6. Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.