Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pekah

29 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. saboda haka Ubangiji yana shirin yă kawo musu rigyawar ruwan Kogi, wato, sarkin Assuriya da dukan sojojinsa. Zai cika dukan gaɓoɓinsa, yă kuma malala har zuwa bakin kogi.

  2. Yă yi ta malala har zuwa cikin Yahuda, yă shafe ta, yana ratsa ta ciki har yă kai kafaɗa. Fikafikansa da ya buɗe za su rufe fāɗin ƙasarka, Ya Immanuwel!”

  3. Ku yi kururuwar yaƙi, ku ƙasashe, ku kuma ji tsoro! Ku saurara, dukanku manisantan ƙasashe. Ku shirya don yaƙi, ku kuma ji tsoro!

  4. Ku ƙirƙiro dabarunku, amma ba za su yi nasara ba; ku ƙulla shirye-shiryenku, amma ba za su yi amfani ba, gama Allah yana tare da mu.