Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Or Copper Brass

7 ayoyi · 43 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.

  2. Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma

  3. da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.

  4. Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.

  5. Suka ɗauke tukwane, da manyan cokula, da acibalbal, da kwanoni, da dai dukan kayan da aka yi da tagulla don hidima a haikalin Ubangiji.

  6. Babban hafsan matsaran sarkin ya kwashe har da kwanoni na kwashe garwashin wuta da sauran kwanoni, dukansu kuwa ƙeran zinariya ko azurfa tsatsa ne.

  7. Tagullar ginshiƙai biyun nan, da ta ƙaton kwanon da ake ce da shi Teku, da ta dukan amalanke masu riƙe ruwa waɗanda Sarki Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji, sun fi gaba a auna su.