Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Milcah

30 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka ’ya’yan Zelofehad mata suka yi yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  2. ’Ya’yan Zelofehad mata, Mala, Tirza, Hogla, Milka da Nowa, suka auri ’ya’yan ’yan’uwa na gefen mahaifinsu.

  3. Suka yi aure cikin kabilar zuriyar Manasse ɗan Yusuf, gādonsu kuwa ya kasance a cikin iyali da kuma kabilar mahaifinsu.

  4. Zelofehad kuwa ɗan Hefer, ɗan Gileyad, ɗan Makir, ɗan Manasse ba shi da ’ya’ya maza, sai dai mata. Ga sunayensu, Mala, Nowa, Hogla, Milka da Tirza.

  5. Suka je wurin Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun, da kuma shugabannin, suka ce musu, “Ubangiji ya umarci Musa cewa yă ba mu gādonmu tare da ’yan’uwanmu maza.” Saboda haka Yoshuwa ya ba su gādo tare da ’yan’uwan mahaifinsu maza bisa ga umarnin Ubangiji.