Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Loaves

18 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, “Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci.”

  2. Yesu ya amsa, “Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci.”

  3. Suka ce, “Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan.”

  4. Ya ce, “Ku kawo mini su a nan.”

  5. Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane.

  6. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

  7. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.

  8. Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”

  9. Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.

  10. Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.

  11. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.

  12. Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.

  13. Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”

  14. Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”

  15. Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”

  16. Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna.

  17. Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.

  18. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.