Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Language: A punishment for presumption, &c

5 ayoyi · 37 fannoni

Ayoyi game da A punishment for presumption, &c

  1. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.

  2. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.

  3. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”

  4. Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.

  5. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.