Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ishmaelites

12 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.

  2. Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa?

  3. Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda.

  4. Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.

  5. Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.

  6. Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”

  7. Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin.

  8. Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”

  9. Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”

  10. Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.

  11. Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.

  12. Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.