Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Egyptians: Aid the Israelites against the Chaldeans

7 ayoyi · 18 fannoni

Ayoyi game da Aid the Israelites against the Chaldeans

  1. Sojojin Fir’auna suka fita daga Masar, sa’ad da Babiloniyawa waɗanda suke ƙawanya wa Urushalima suka ji labari game da su, sai suka janye daga Urushalima.

  2. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya annabi cewa,

  3. “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana cewa ka faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aika a neme ni cewa, ‘Sojojin Fir’aunan da suka fito su taimake ka, za su koma ƙasarsu, Masar.

  4. Sa’an nan Babiloniyawa za su koma su yaƙi wannan birni su ci ta su kuma ƙone shi.’

  5. “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku ruɗe kanku, kuna tsammani, ‘Tabbatacce Babiloniyawa sun bar mu.’ Ba za su bari ba!

  6. Ko da a ce za ku ci dukan sojojin Babiloniyawan da suke yaƙi da ku har raunana ne kawai aka bari a tentunansu, za su fito su ƙone wannan birni.”

  7. Bayan sojojin Babiloniyawa suka janye daga Urushalima saboda sojojin Fir’auna,