Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Curtains: For tabernacle

21 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da For tabernacle

  1. “Ka yi fili domin tabanakul. Tsawon gefen kudu zai zama kamu ɗari da labulen da aka yi da zaren lili mai kyau,

  2. da katakai ashirin da rammukan tagulla ashirin da ƙugiyoyin azurfa da kuma rammuka a kan katakai.

  3. A wajen arewa shi ma, tsawon yă zama ƙafa ɗari. Ka kama labulen da ƙugiyoyin da aka yi da azurfa waɗanda aka manna a kan ƙarfen da aka dalaye da azurfa.

  4. “Faɗin ƙarshen filin a yamma zai zama kamu hamsin. A kuma sa labule tare da rammuka goma da kuma katakai goma.

  5. A wajen gabas can ƙarshe, wajen fitowar rana, fāɗin filin zai zama kamu hamsin.

  6. Tsayin labulen ƙofa na gefe ɗaya zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku,

  7. haka kuma tsayin labule na wancan gefen, zai zama kamu goma sha biyar, da katakai uku tare da rammukansu uku.

  8. “Domin ƙofar tentin, a saƙa labule mai tsayin kamu ashirin da lallausan zaren lilin mai ruwan shuɗi, da shunayya, da jan zare, mai aikin gwani, da katakai huɗu tare da rammukansu huɗu.

  9. Duk katakan da suke kewaye da filin, za a yi musu maɗaurai na azurfa da kuma ƙugiyoyi, da rammukan tagulla.

  10. Tsayin filin zai zama kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu hamsin, tsayin labulensa na lallausan zaren lilin zai zama kamu biyar, a kuma yi rammukansa da tagulla.

  11. Dukan maza masu fasaha a cikin sauran masu aikin suka yi tabanakul da labule goma na tuƙaƙƙun lallausan lilin na shuɗi, da shunayya, da jan zare, aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.

  12. Tsawon kowane labule, kamu ashirin da takwas ne, fāɗinsa kuma kamu huɗu. Dukan labulen, girmansu ɗaya ne.

  13. Suka ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, suka kuma yi haka da sauran labule biyar ɗin.

  14. Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin.

  15. Suka kakkafa rammuka hamsin a daidai bakin labulen, haka kuma suka yi a kan labule na biyun. Haka aka ɗaɗɗaura rammukan nan da junansu yă zama kamar abu guda.

  16. Sa’an nan suka yi maɗaurai hamsin na zinariya, suka yi amfani da su don daurin kashi biyu na labulen saboda tabanakul yă zama ɗaya.

  17. Suka yi labule da gashi akuya goma sha ɗaya don tenti a bisa tabanakul.

  18. Dukan labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne, tsawonsa kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne.

  19. Suka harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, suka kuma harhaɗa shida wuri ɗaya.

  20. Sa’an nan suka yi rammuka hamsin a gefen labule na kashe na farko, haka kuma a gefen labule na ƙarshen na kashi biyar.

  21. Suka yi maɗaurin tagulla hamsin don su ɗaura tenti yă zama ɗaya.