Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Christ is God: As Jehovah, the First and the Last

5 ayoyi · 55 fannoni

Nemi "Christ is God"

Ayoyi game da As Jehovah, the First and the Last

  1. “Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe.

  2. Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.

  3. “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa.

  4. Ni kaina, na faɗa; I, na kira shi. Zan kawo shi, zai kuma yi nasara a cikin aikinsa.

  5. “Ku zo kusa da ni ku kuma saurari wannan. “Daga farkon shela ban yi magana a ɓoye ba; a lokacin da ya faru, ina nan a wurin.” Yanzu kuwa Ubangiji Mai Iko Duka ya aiko ni, da Ruhunsa.