Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Christ is God: As the Eternal God and Creator

7 ayoyi · 55 fannoni

Ayoyi game da As the Eternal God and Creator

  1. Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.

  2. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

  3. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.

  4. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.

  5. Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

  6. Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga.

  7. Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”