Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Bride: Figurative

17 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Figurative

  1. Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.

  2. Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.

  3. Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.

  4. Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya.

  5. Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.

  6. Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.

  7. ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.

  8. Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.

  9. “ ‘Daga baya na wuce, da na dube ki sai na ga cewa kin yi girma sosai har kin kai a ƙaunace ki, na yafa gefen tufafina a kanki na kuma rufe tsiraincinki. Na rantse miki, na ƙulla alkawari da ke, kin kuwa zama tawa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  10. “ ‘Na yi miki wanka na wanke miki jini daga gare ki na kuma shafa miki mai.

  11. Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.

  12. Na yi miki ado da kayan ado masu daraja, na sa miki mundaye a hannuwanki da abin wuya a wuyanki,

  13. na kuma sa miki zobe a hancinki, abin kunne a kunnuwanki da rawani mai kyau a kanki.

  14. Haka kuwa aka caɓa miki zinariya da azurfa; tufafinki kuwa na lilin mai kyau da riguna masu tsada waɗanda aka yi musu ado. Abincinki na gari mai laushi ne, zuma da man zaitun. Kika zama kyakkyawa har kika kuma zama sarauniya.

  15. Sunanki ya yaɗu a cikin al’ummai saboda kyanki, domin darajar da na ba ki ya sa kyanki ya zama cikakke, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  16. Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta.

  17. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.)