Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Avenger of Blood: Scriptures relating to

32 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Scriptures relating to

Tace bisa littafi
  1. Game da jinin ranka kuwa lalle zan bukaci lissafi. Zan bukaci lissafi daga kowane dabba. kuma daga kowane mutum, shi ma zan bukaci lissafi game da ran ɗan’uwansa.

  2. “Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.

  3. Sai mai bin hakkin jinin yă kashe mai kisankan, sa’ad da ya sadu da mai kisankan, sai yă kashe shi.

  4. In saboda ƙiyayya, mutum ya laɓe, ya soke wani, ko ya jefe shi da wani abu da gangan har ya mutu,

  5. ko kuwa saboda ƙiyayya ya naushe shi har ya mutu, sai a kashe wannan mutumin da ya yi haka; shi mai kisankai ne. Sai mai bin hakkin jini yă kashe mai kisankan in ya same shi.

  6. “ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,

  7. ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,

  8. dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.

  9. Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.

  10. “ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,

  11. idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.

  12. Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.

  13. “ ‘Waɗannan su ne za su zama ƙa’idodin da za ku kasance da su, a dukan tsararraki masu zuwa.

  14. Ga doka game da mutumin da ya kashe wani, ya kuma gudu don yă cece ransa, wani wanda ya kashe maƙwabcinsa ba da gangan ba, ba kuwa da wata ƙiyayya a tsakaninsu a dā ba.

  15. Misali, in mutum ya je jeji da maƙwabcinsa domin yankan itace, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe daga ƙotar yayinda yake saran itacen, ya sari maƙwabcin har ya mutu. Mutumin nan zai iya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane don yă ceci ransa.

  16. In ba haka ba mai neman ɗaukan fansa jini, zai iya binsa cikin fushi, yă cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā.

  17. Wannan ne ya sa na umarce ku ku keɓe wa kanku birane uku.

  18. In Ubangiji Allahnku ya fadada yankinku, kamar yadda ya alkawarta da rantsuwa wa kakanninku, ya kuma ba ku ƙasar gaba ɗaya kamar yadda ya yi musu alkawari,

  19. idan dai kun lura, kuka kiyaye umarnin da nake ba ku a yau, wato, ta wurin ƙaunar Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya kullum cikin hanyoyinsa, to, sai ku keɓe ƙarin birane uku.

  20. Ku yi haka don kada a zub da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, don kada ku kuma zama masu laifin zub da jini.

  21. Amma idan wani mutum yana ƙin maƙwabcinsa, ya kuma yi kwanto yana fakonsa, ya yi masa rauni, har ya kashe shi, sa’an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane,

  22. dattawan garinsa za su aika a kawo shi, a dawo da shi daga birnin, a miƙa shi ga mai neman fansar jini don yă kashe shi.

  23. Kada ku ji tausayinsa. Dole ku fid da laifin zub da jinin marar laifi daga Isra’ila, don ku sami zaman lafiya.

  24. Sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,

  25. “Ka gaya wa Isra’ilawa su keɓe waɗansu birane su zama biranen mafaka kamar yadda na umarce ku ta wurin Musa,