Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Anointing: Symbolic, of Jesus

11 ayoyi · 32 fannoni

Ayoyi game da Symbolic, of Jesus

  1. wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.

  2. Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa!

  3. Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.”

  4. Sane da wannan, Yesu ya ce musu, “Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.

  5. Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.

  6. Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata.

  7. Sai Maryamu ta ɗauki wajen awo guda na nardi zalla, turare mai tsada; ta zuba a ƙafafun Yesu ta kuma goge ƙafafunsa da gashinta. Gidan duk ya cika da ƙanshin turaren.

  8. Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce,

  9. “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.”

  10. Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki.

  11. Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata.