Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ahitub

13 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A cikinsu akwai Ahiya sanye da efod. Shi yaron Ikabod ɗan’uwan Ahitub ne, ɗan Finehas, ɗan Eli, firist na Ubangiji a Shilo. Ba wanda ya san cewa Yonatan ya tafi wani wuri.

  2. Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob.

  3. Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki.

  4. Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.” Ya amsa ya ce, “Ina saurara, ranka yă daɗe.”

  5. Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda.

  6. Zadok ɗan Ahitub da Ahimelek ɗan Abiyatar, su ne firistoci; Serahiya kuma sakatare;

  7. Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz,

  8. Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,

  9. Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,

  10. Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;

  11. Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;

  12. sai Azariya babban firist, daga iyalin Zadok ya amsa, “Tun daga lokacin da mutane suka fara kawo taimakonsu ga haikalin Ubangiji, muna da isashe don abinci da kuma da yawa da za mu rage, domin Ubangiji ya albarkaci mutanensa, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”

  13. da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,