Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Agency

37 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta wurin ziyarar Yoram, Allah ya kawo fāɗuwar Ahaziya. Sa’ad da Ahaziya ya iso, ya tafi tare da Yoram domin yă sadu da Yehu ɗan Nimshi, wanda Ubangiji ya shafe don yă hallaka gidan Ahab.

  2. Ka tashi, ya Ubangiji, ka yi arangama da su, ka durƙusar da su; ka cece ni daga mugaye ta wurin takobinka.

  3. Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.

  4. “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!

  5. Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.

  6. Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar.

  7. “Duba, zan sa ka cikin abin sussuka, saboda kuma mai kaifi mai haƙora da yawa. Za ka yi sussukar duwatsu ka ragargaza su, ka kuma farfashe tuddai su zama kamar yayi.

  8. “ ‘ “Amma fa, duk al’umma ko mulkin da bai bauta wa Nebukadnezzar sarkin Babilon ba bai kuwa rusunar da wuyarsa ga karkiyarsa ba, zan hukunta wannan al’umma da takobi, yunwa da annoba, in ji Ubangiji, har sai na hallaka ta ta wurin hannunsa.

  9. “Kai ne kulkin yaƙina, kayan yaƙina, da kai ne na ragargaza ƙasashe, da kai ne na hallaka mulkoki,

  10. da kai ne na ragargaza doki da mahayi, da kai ne na ragargaza keken yaƙin da matuƙi,

  11. da kai ne na ragargaza miji da mata, da kai ne na ragargaza tsoho da saurayi, da kai ne na ragargaza saurayi da budurwa,

  12. da kai ne na ragargaza makiyayi da garke, da kai ne na ragargaza manoma da dawakan noma, da kai ne na ragargaza masu mulki da shugabanni.