Skip to content
Waƙar Waƙoƙi 2:1-8

Waƙar Waƙoƙi 2:1-8

1
Ni furen bi-rana ne na Sharon, furen bi-rana na kwari.
2
Kamar furen bi-rana a cikin ƙayayyuwa haka ƙaunatacciyata take a cikin ’yan mata.
3
Kamar itacen gawasa a cikin itatuwan jeji haka ƙaunataccena yake a cikin samari. Ina farin ciki in zauna a inuwarsa, ’ya’yan itacensa suna da daɗin ɗanɗanon da nake so
4
Ya kai ni babban zauren da ake liyafa, ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.
5
Ka ƙarfafa ni da zabibi ka wartsake ni da gawasa, gama ina suma don ƙauna.
6
Hannunsa na hagu yana a ƙarƙashin kaina, hannunsa na dama kuma ya rungume ni.
7
’Yan matan Urushalima, ku yi mini alkawari da bareyi da ƙishimai na jeji. Ba za ku tā da ko ku farka ƙauna ba sai haka ya zama lalle.
8
Saurara! Ƙaunataccena! Duba! Ga shi ya iso, yana tsalle a duwatsu, yana rawa a bisa tuddai.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options