Przejdź do treści
Ru’uya ta Yohanna 22:1-14

Ru’uya ta Yohanna 22:1-14

1
Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon,
2
yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne.
3
Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima.
4
Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu.
5
Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.
6
Mala’ikan ya ce mini, “Waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa, ya aiki mala’ikansa, don yă nuna wa bayinsa abubuwan da za su faru nan ba da daɗewa ba.”
7
“Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.”
8
Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada.
9
Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!”
10
Sa’an nan ya gaya mini cewa, “Kada ka rufe kalmomin annabcin littafin nan, domin lokaci ya yi kusa.
11
Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
12
“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.
13
Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.
14
“Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options