Skip to content
Ru’uya ta Yohanna 22:18-21

Ru’uya ta Yohanna 22:18-21

18
Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan.
19
Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.
20
Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu!
21
Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options