Skip to content
Zabura 69:7-21

Zabura 69:7-21

7
Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.
8
Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;
9
gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.
10
Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;
11
sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.
12
Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.
13
Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.
14
Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.
15
Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina.
16
Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.
17
Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.
18
Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana.
19
Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.
20
Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.
21
Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options