Zabura 44:9-22
9
Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
10
Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.
11
Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.
12
Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.
13
Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
14
Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.
15
Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya
16
saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.
17
Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
18
Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
19
Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.
20
Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
21
da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?
22
Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
Settings