Mattiyu 24:3-14
3
Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”
4
Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.
5
Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.
6
Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.
7
Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.
8
Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.
9
“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.
10
A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,
11
annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.
12
Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,
13
amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.
14
Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
Settings