Skip to content
Markus 14:1-15

Markus 14:1-15

1
To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
2
Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”
3
Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.
4
Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka?
5
Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”
6
Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.
7
Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.
8
Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata.
9
Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”
10
Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su.
11
Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.
12
A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
13
Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi.
14
Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’
15
Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options