Skip to content
Luka 20:16-40

Luka 20:16-40

16
Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.” Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”
17
Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’
18
Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
19
Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
20
Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.
21
Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.
22
Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
23
Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,
24
“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?” Suka amsa, “Na Kaisar.”
25
Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
26
Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
27
Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,
28
“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’
29
To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya.
30
Na biyun,
31
da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya.
32
A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.
33
Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
34
Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure,
35
amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.
36
Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.
37
Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’
38
Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
39
Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!”
40
Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options