Luka 1:52-76
52
Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.
53
Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.
54
Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai
55
ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”
56
Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.
57
Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.
58
Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.
59
A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne,
60
amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”
61
Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”
62
Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron.
63
Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.
64
Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.
65
Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya.
66
Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.
67
Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,
68
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.
69
Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda
70
(yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
71
cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu
72
don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
73
rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,
74
don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,
75
cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.
76
“Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,
Settings