Yoshuwa 21:21-45
21
A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer,
22
Kibzayim da Bet-Horon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.
23
Haka kuma daga kabilar Dan, aka ba su, Elteke, Gibbeton,
24
Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.
25
Daga rabin kabilar Manasse kuwa aka ba su, Ta’anak da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan.
26
Dukan garuruwan nan goma tare da wuraren kiwonsu ne aka ba sauran iyalan Kohatawa.
27
Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan;
28
daga kabilar Issakar kuma aka ba su Kishiyon, Daberat,
29
Yarmut da En Gannim, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
30
daga kabilar Asher kuwa aka ba su, Mishal, Abdon,
31
Helkat da Rehob, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
32
daga kabilar Naftali kuma aka ba su, Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan.
33
Duka-duka, garuruwan iyalan Gershonawa goma sha uku ne, tare da wuraren kiwonsu.
34
Aka ba wa iyalan Merari (sauran Lawiyawa) garuruwa, daga kabilar Zebulun, wato, Yokneyam, Karta,
35
Dimna da kuma Nahalal, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
36
daga kabilar Ruben kuma aka ba su, Bezer, Yahza,
37
Kedemot da kuma Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;
38
daga kabilar Gad kuwa aka ba su, Ramot Gileyad (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Mahanayim,
39
Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.
40
Duka-duka garuruwan da aka ba iyalan mutanen Merari, waɗanda su ne sauran Lawiyawa, garuruwa goma sha biyu ne.
41
Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne.
42
Dukan garuruwan nan kowannensu yana kewaye da wurin kiwo.
43
Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya yi wa kakanninsu alkawari, suka kuwa mallake ta, suka zauna a cikinta.
44
Ubangiji ya ba su hutawa a kowane gefe kamar yadda ya yi wa kakanninsu alkawari, ba ko ɗaya daga cikin abokan gābansu da ya iya cinsu da yaƙi.
45
Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alherin da ya yi wa mutanen Isra’ila.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings