Skip to content
Yohanna 6:26-69

Yohanna 6:26-69

26
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.
27
Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”
28
Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”
29
Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”
30
Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?
31
Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’”
32
Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.
33
Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”
34
Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”
35
Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
36
Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
37
Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
38
Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
39
Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
40
Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
41
Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
42
Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”
43
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
44
Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
45
A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
46
Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
47
Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
48
Ni ne burodin rai.
49
Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.
50
Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
51
Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”
52
Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”
53
Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.
54
Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
55
Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56
Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.
57
Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.
58
Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.”
59
Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.
60
Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”
61
Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?
62
Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!
63
Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.
64
Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65
Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”
66
Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
67
Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”
68
Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.
69
Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options