Yohanna 6:35-50
35
Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.
36
Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.
37
Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.
38
Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.
39
Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.
40
Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”
41
Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”
42
Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”
43
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.
44
Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.
45
A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.
46
Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.
47
Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.
48
Ni ne burodin rai.
49
Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.
50
Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.
Settings