Skip to content
Yohanna 19:30-42

Yohanna 19:30-42

30
Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
31
To, ranan nan fa, ranar Shirye-shirye ce, kashegari kuma muhimmin Asabbaci ne. Domin Yahudawa ba sa so a bar jikunan a kan gicciyoyi a Asabbaci, sai suka roƙi Bilatus a kakkarye ƙafafunsu kuma sauko da jikunan.
32
Sai sojoji suka zo suka karya ƙafafun mutum na farko da aka gicciye tare da Yesu, da kuma na ɗayan.
33
Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.
34
A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito.
35
Mutumin da ya gani ɗin shi ya ba da shaida, shaidarsa kuwa gaskiya ce. Ya san gaskiya yake faɗa, yana kuma ba da shaidar domin ku ma ku gaskata.
36
Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,”
37
kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
38
Bayan haka, Yusuf mutumin Arimateya ya roƙi Bilatus a ba shi jikin Yesu. Yusuf dai almajirin Yesu ne, amma a ɓoye domin yana tsoron Yahudawa. Da izinin Bilatus, ya zo ya ɗauki jikin.
39
Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari.
40
Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza.
41
A inda aka gicciye Yesu, akwai wani lambu, a cikin lambun kuwa akwai sabon kabari, wanda ba a taɓa sa kowa ba.
42
Da yake ranan nan, ranar Shirye-shirye ce ta Yahudawa, kabarin kuma yana kusa, sai suka binne Yesu a can.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options