Skip to content
Irmiya 49:7-22

Irmiya 49:7-22

7
Game da Edom. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Babu sauran hikima a Teman ne? Shawara ta ɓace daga masu basira ne? Hikimarsu ta ruɓe ne?
8
Ku juya ku gudu, ku ɓuya a cikin kogwanni masu zurfi, ku da kuke zama a Dedan, gama zan kawo masifa a kan Isuwa a lokacin da zan hukunta shi.
9
In masu tsinkar ’ya’yan inabi suka zo maka, ba za su rage ’ya’yan inabi kaɗan ba? In ɓarayi suka zo da dare, ba za su sata abin da kawai suke bukata ba?
10
Amma zan washe Isuwa sarai; zan bubbuɗe wuraren ɓuyarsa, don kada yă ɓoye kansa. ’Ya’yansa, danginsa da maƙwabtansa za su hallaka, ba kuwa zai ƙara kasancewa ba.
11
Ka bar marayunka; zan tsare ransu. Gwaurayenka kuma za su dogara a gare ni.”
12
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In waɗanda ba su dace su sha kwaf ɗin ba suka sha shi, me ya sa za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, sai ka sha shi.
13
Na rantse da kaina,” in ji Ubangiji, “cewa Bozra za tă zama kufai da kuma abin tsoro, abin dariya da abin la’ana; kuma dukan garuruwanta za su kasance kufai har abada.”
14
Na ji saƙo daga Ubangiji cewa; an aiki jakada zuwa ga al’ummai ya ce, “Ku tattara kanku don ku fāɗa mata! Ku tashi don yaƙi!”
15
“Yanzu zan mai da kai ƙanƙani a cikin al’ummai abin reni a cikin mutane.
16
Tsoron da ka sa ake ji da kuma girman kan zuciyarka ya ruɗe ka, kai da kake zama a kogon dutse, kai da kake kan tudu. Ko da yake ka gina wa kanka sheƙa can bisa kamar na gaggafa, daga can zan sauko da kai ƙasa,” in ji Ubangiji.
17
“Edom za tă zama abin tsoro; dukan wanda ya wuce zai giggice ya yi tsaki saboda dukan mikinta.
18
Kamar yadda aka tumɓuke Sodom da Gomorra, tare da garuruwan da suke maƙwabtaka da su,” in ji Ubangiji, “haka ba wanda zai zauna a can; ba wani da zai zauna a cikinta.
19
“Kamar zaki mai haurawa daga kurmin Urdun zuwa wurin kiwo mai kyau, zan kori Edom daga ƙasarta nan da nan. Wane ne zaɓaɓɓen da zan naɗa don wannan? Wane ne yake kama da ni kuma wa zai kalubalance ni? Kuma wane makiyayi ne zai yi gāba da ni?”
20
Saboda haka, ku ji abin da Ubangiji ya shirya a kan Edom, abin da ya nufa wa waɗanda suke zama a Teman. Za a ja ƙanana na garken tumaki a tafi; zai hallaka wurin kiwonsu sarai saboda su.
21
Amon fāɗuwarsu zai sa ƙasa ta girgiza; za a kuma ji muryar kukansu a Jan Teku.
22
Duba! Gaggafa tana firiya tana kuma saukowa, tana buɗe fikafikanta a bisa Bozra. A wannan rana zukatan jarumawan Edom za su zama kamar macen da take naƙuda.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options