Irmiya 49:1-6
1
Game da Ammonawa. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Isra’ila ba shi da ’ya’ya maza ne? Ba shi da magāda ne? To, me ya sa Molek ya mallaki Gad? Me ya sa mutanensa suka zama a garuruwansa?
2
Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi kirarin yaƙi a kan Rabba ta Ammonawa; zai zama tarin juji, za a sa wuta a ƙauyukan da suke kewayenta. Sa’an nan Isra’ila zai kori waɗanda suka kore shi,” in ji Ubangiji.
3
“Ki yi kuka, ya Heshbon, gama an hallaka Ai! Ku tā da murya ku yi kuka, ya mazaunan Rabba! Ku sa tufafin makoki; ku ruga nan da can a cikin katanga, gama Molek zai tafi bauta, tare da firistocinsa da kuma fadawansa.
4
Me ya sa kuke taƙama da kwarurukanku, taƙama da kwarurukanku masu amfani? Ya ke diya marar aminci, kin dogara a wadatarki kika kuma ce, ‘Wa zai iya fāɗa mini?’
5
Zan kawo razana a kanki daga waɗanda suke kewaye da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Za a kore kowannenku, babu wani da zai tattara masu gudun hijira.
6
“Duk da haka, daga baya, zan maido da wadatar Ammonawa,” in ji Ubangiji.
Settings