Farawa 35:1-15
1
Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”
2
Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku.
3
Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.”
4
Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem.
5
Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.
6
Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana.
7
A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.
8
To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.
9
Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi.
10
Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.
11
Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.
12
Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”
13
Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.
14
Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa.
15
Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.
Settings