Skip to content
Farawa 30:1-24

Farawa 30:1-24

1
Sa’ad da Rahila ta ga cewa ba tă haifa wa Yaƙub ’ya’ya ba, sai ta fara kishin ’yar’uwarta. Saboda haka ta ce wa Yaƙub, “Ka ba ni ’ya’ya, ko kuwa in mutu!”
2
Yaƙub ya fusata da ita ya ce, “Ina a matsayin Allah ne wanda ya hana ke samun ’ya’ya?”
3
Sa’an nan ta ce, “Ga Bilha, mai baiwata, ka kwana da ita don tă haifa mini ’ya’ya, ta gare ta kuwa ni ma in gina iyali.”
4
Saboda haka ta ba shi baranyarta Bilha tă zama matarsa. Yaƙub kuwa ya kwana da ita,
5
ta kuwa yi ciki, ta kuma haifi ɗa.
6
Sa’an nan Rahila ta ce, “Allah ya baratar da ni; ya saurari roƙona ya kuma ba ni ɗa.” Saboda wannan ta ba shi suna Dan.
7
Baranyar Rahila ta sāke yin ciki ta kuma haifi wa Yaƙub ɗa na biyu.
8
Sai Rahila ta ce, “Na yi kokawa sosai da ’yar’uwata, na kuwa yi nasara.” Saboda haka ta kira shi Naftali.
9
Sa’ad da Liyatu ta ga cewa ta daina haihuwa, sai ta ɗauki mai hidimarta Zilfa ta ba da ita ga Yaƙub tă zama matarsa.
10
Baranyar Liyatu, Zilfa ta haifa wa Yaƙub ɗa.
11
Sai Liyatu ta ce, “Na yi sa’a!” Saboda haka ta ba shi suna Gad.
12
Zilfa baranyar Liyatu ta haifa wa Yaƙub ɗa na biyu.
13
Sai Liyatu ta ce, “Ni mai farin ciki ce! Mata za su ce da ni mai farin ciki.” Saboda haka ta sa masa suna Asher.
14
A lokacin girbin alkama, sai Ruben ya je jeji ya ɗebo manta-uwa ya kawo wa mahaifiyarsa Liyatu. Sai Rahila ta ce wa Liyatu, “Ina roƙonki ki ɗan sam mini manta-uwa ɗanki.”
15
Amma ta ce mata, “Bai ishe ki ba ne da kika ƙwace mijina? Yanzu kuma kina so ki ƙwace manta-uwa na yarona?” Sai Rahila ta ce “Shi ke nan, mijina zai iya kwana da ke yau saboda manta-uwa na ɗanki.”
16
Saboda haka sa’ad da Yaƙub ya dawo daga jeji a wannan yamma sai Liyatu ta fito ta tarye shi. Ta ce, “Dole ka kwana da ni, na yi hayarka da manta-uwa na ɗana.” Saboda haka ya kwana da ita a wannan dare.
17
Allah ya saurari Liyatu, ta kuwa yi ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na biyar.
18
Sai Liyatu ta ce, “Allah ya sāka mini saboda na ba da mai hidimata ga mijina.” Saboda haka ta ba shi suna Issakar.
19
Liyatu ta sāke yin ciki ta kuma haifa wa Yaƙub ɗa na shida.
20
Sai Liyatu ta ce, “Allah ya ba ni kyauta mai daraja. A wannan lokaci mijina zai darajarta ni, domin na haifa masa ’ya’ya maza shida.” Saboda haka ta ba shi suna Zebulun.
21
Daga baya ta haifi ’ya ta kuwa ba ta suna Dina.
22
Sai Allah ya tuna da Rahila; ya saurare ta ya kuma buɗe mahaifarta.
23
Sai ta yi ciki ta kuma haifi ɗa ta ce, “Allah ya ɗauke mini kunyata.”
24
Ta ba shi suna Yusuf, ta kuma ce, “Bari Ubangiji yă ƙara mini wani ɗa.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options