Fitowa 36:20-30
20
Suka yi katakan tabanakul da itacen ƙirya.
21
Tsawon kowane katako kamu goma ne, kaurinsa kuma kamu ɗaya da rabi,
22
tare da katakai a fiƙe ɗaura da juna. Haka suka yi da dukan katakan tabanakul.
23
Suka yi katakai ashirin don gefen kudu na tabanakul
24
suka kuma yi rammukan azurfa arba’in don katakan su shiga ƙarƙashinsu, rammuka biyu domin kowane katako, ɗaya ƙarƙashin kowanne da aka fiƙe.
25
A ɗaya gefen, gefen arewa na tabanakul, suka yi katakai ashirin
26
da rammuka arba’in na azurfa, biyu-biyu don kowane katako.
27
Suka yi katako shida don iyaka ta ƙarshe, wato, gefen yamma na tabanakul,
28
aka kuma yi katakai biyu domin kusurwoyi tabanakul a iyaka ta ƙarshe.
29
A waɗannan kusurwoyi biyu, an ninka katakan sau biyu daga ƙasa har sama, aka kuma sa su cikin zobe guda; dukansu biyu an yi su daidai.
30
Ta haka aka sami katakai takwas da rammukan azurfa goma sha shida, biyu-biyu a ƙarƙashin kowane katako.
Settings