Skip to content
Fitowa 36:14-19

Fitowa 36:14-19

14
Suka yi labule da gashi akuya goma sha ɗaya don tenti a bisa tabanakul.
15
Dukan labule goma sha ɗayan girmansu ɗaya ne, tsawonsa kamu talatin, fāɗinsa kuma kamu huɗu ne.
16
Suka harhaɗa labule biyar wuri ɗaya, suka kuma harhaɗa shida wuri ɗaya.
17
Sa’an nan suka yi rammuka hamsin a gefen labule na kashe na farko, haka kuma a gefen labule na ƙarshen na kashi biyar.
18
Suka yi maɗaurin tagulla hamsin don su ɗaura tenti yă zama ɗaya.
19
Sai suka yi wa tentin murfi da fatun rago da aka rina ja, a bisa wannan kuwa akwai murfin fatun shanun teku.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options