Fitowa 36:8-13
8
Dukan maza masu fasaha a cikin sauran masu aikin suka yi tabanakul da labule goma na tuƙaƙƙun lallausan lilin na shuɗi, da shunayya, da jan zare, aka yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta.
9
Tsawon kowane labule, kamu ashirin da takwas ne, fāɗinsa kuma kamu huɗu. Dukan labulen, girmansu ɗaya ne.
10
Suka ɗinɗinke labule biyar a harhaɗe, suka kuma yi haka da sauran labule biyar ɗin.
11
Suka yi rami a gefe-gefen labulen da zaren ruwan bula, haka kuma suka yi da ɗayan gefen na biyu ɗin.
12
Suka kakkafa rammuka hamsin a daidai bakin labulen, haka kuma suka yi a kan labule na biyun. Haka aka ɗaɗɗaura rammukan nan da junansu yă zama kamar abu guda.
13
Sa’an nan suka yi maɗaurai hamsin na zinariya, suka yi amfani da su don daurin kashi biyu na labulen saboda tabanakul yă zama ɗaya.
Settings