Skip to content
Fitowa 15:13-27

Fitowa 15:13-27

13
A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe mutanen da ka fansa. A cikin ƙarfinka, za ka bishe su zuwa mazauninka mai tsarki.
14
Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki tsoro zai kama mutanen Filistiya.
15
Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.
16
Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.
17
Za ka kawo su, ka dasa su a kan dutsen nan naka inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka, wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.
18
“Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”
19
Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
20
Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.
21
Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji gama ya ci gawurtacciyar nasara. Doki da mahayi, ya jefa cikin teku.”
22
Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.
23
Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).
24
Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”
25
Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su.
26
Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
27
Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options