Esta 9:1-19
1
A rana ta goma sha uku na watan goma sha biyu, wato, watan Adar ne za a aiwatar da dokar da sarki ya umarta. A wannan rana, abokan gāban Yahudawa suka sa zuciya za su sha ƙarfinsu, amma yanzu Zerzes ya canja, Yahudawa kuma suka yi galiba a bisa waɗanda suka ƙi jininsu.
2
Yahudawa suka tattaru a cikin biranensu a dukan lardunan Sarki Zerzes don su kai wa waɗanda suka nemi a hallaka su hari. Babu wanda ya tasar musu domin mutanen dukan sauran al’ummai sun jin tsoronsu.
3
Dukan sarakuna larduna, da hakimai, da gwamnoni da kuma ma’aikatan sarki suka taimaki Yahudawa, domin tsoron Mordekai ya kama su.
4
Mordekai babban mutum ne a fada, sunansa ya kai ko’ina a lardunan, ikonsa ya yi ta ƙasaita gaba-gaba.
5
Yahudawa suka karkashe dukan abokan gābansu da takobi, suka karkashe waɗanda suka ƙi jininsu, suka kuma hallaka su yadda suka ga dama.
6
A mazaunin masarautar a Shusha, Yahudawa suka karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar.
7
Suka kuma kashe Farshandata, da Dalfon, da Asfata,
8
da Forata, da Adaliya, da Aridata,
9
da Farmashta, da Arisai, da Aridai da kuma Baizata,
10
’ya’ya maza goma na Haman ɗan Hammedata, abokin gāban Yahudawa. Amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
11
A wannan rana, aka ba wa sarki rahoton yawan mutanen da aka kashe a mazaunin masarauta, a Shusha.
12
Sarki ya ce wa Sarauniya Esta, “Yahudawa sun karkashe, suka kuma hallaka mutum ɗari biyar, da kuma ’ya’ya maza goma na Haman a mazaunin masarauta a Shusha. Me suka yi a sauran lardunan sarki? Yanzu kuma mene ne roƙonki? Za a ba ki. Mece ce bukatarki? Za a biya miki.”
13
Esta ta ce, “In sarki ya yarda, yă ba wa Yahudawa da suke Shusha izini su aikata dokan nan gobe kuma, bari kuma a rataye ’ya’ya maza goma na Haman a kan gumagumai.”
14
Sai sarki ya ba da umarni a yi haka ɗin. Aka ba da doka a Shusha, aka kuma rataye ’ya’ya maza goma na Haman.
15
Yahudawan da suke Shusha suka taru a ran goma sha huɗu na watan Adar suka kuma karkashe mutum ɗari uku a Shusha, amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
16
Ana cikin haka, sai saura Yahudawa waɗanda suke lardunan sarki su ma suka taru domin su kāre kansu su kuma sami hutu daga abokan gābansu. Suka karkashe mutum dubu saba’in da biyar amma ba su taɓa dukiyarsu ba.
17
Wannan ya faru a ran goma sha uku na watan Adar. A rana ta goma sha huɗu kuwa suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da kuma ta farin ciki.
18
Amma Yahudawan da suke a Shusha suka taru a rana ta goma sha uku da ta sha huɗu, sa’an nan a rana ta goma sha biyar suka huta, suka kuma mai da ita ranar biki da ta farin ciki.
19
Shi ya sa Yahudawan ƙauyuka, waɗanda suke zama a karkara, suke kiyaye rana ta goma sha huɗu ta watan Adar a matsayin ranar farin ciki da ta biki, ranar ba da kyautai ga juna.
Settings