Skip to content
Daniyel 2:3-27

Daniyel 2:3-27

3
sai ya ce musu, “Na yi mafarkin da ya dame ni kuma ina so in san me yake nufi.”
4
Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki da Arameyanci “Ran sarki yă daɗe! Ka faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma sai mu fassara.”
5
Sai sarki ya amsa wa masanan taurarin ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa-gunduwa, a mai da gidajenku juji.
6
Amma in har kuka faɗa mini mafarkina kuka kuma bayyana fassararsa, za ku sami lada mai girma. Saboda haka ku faɗa mini mafarkin da kuma fassararsa.”
7
Sai suka sāke amsa masa suka ce, “Ran sarki yă daɗe, faɗa wa bayinka mafarkin, mu kuma za mu fassara shi.”
8
Sai sarki ya amsa ya ce, “Na gane cewa kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin ku ga na manta da abin.
9
In ba ku faɗa mini mafarkin ba, akwai hukunci guda ɗaya kurum dominku. Kun haɗa baki domin ku faɗa mini munanan al’amura domin ku ruɗe ni har lokaci yă wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”
10
Sai masanan taurarin suka amsa wa sarki suka ce, “Babu wani mutum a duniyan nan da zai iya yin abin da sarki yake nema! Babu wani sarki mai daraja da girma wanda ya taɓa yin irin wannan tambaya ga masu sihiri ko masu dabo ko masanan taurari.
11
Abin da sarki yake nema yana da wuya matuƙa. Babu wani da zai iya bayyana wannan ga sarki sai dai alloli; kuma ba su zama tare da ’yan adam.”
12
Wannan ya sa sarki ya fusata ƙwarai, ya ba da umarni a tafi da dukan masu hikima na Babilon a kashe su.
13
Sai aka ba da dokar da za a kashe masu hikima, sa’an nan aka aika mutane su je su nemo Daniyel da abokansa domin a kashe su.
14
Sa’ad da Ariyok, shugaban ƙungiyar matsaran sarki, ya fita domin yă kashe masu hikima na Babilon, sai Daniyel ya yi masa magana cikin hikima da dabara.
15
Ya tambayi mai tsaro na sarki, “Me ya sa sarki ya fitar da wannan doka haka da fushi?” Sai Ariyok ya yi wa Daniyel bayanin batun.
16
Da jin haka sai Daniyel ya tafi wurin sarki ya nemi ƙarin lokaci, domin yă bayyana wa sarki mafarkin da kuma fassararsa.
17
Sa’an nan Daniyel ya komo gida ya kuma sanar wa abokansa Hananiya, Mishayel da Azariya, batun nan duka.
18
Ya roƙe su su roƙi jinƙan Allah na sama domin wannan mafarki, saboda kada a kashe shi da abokansa tare da sauran masu hikima na Babilon.
19
A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama.
20
Ya ce, “Yabo ya tabbata ga sunan Allah har abada abadin; hikima da iko nasa ne.
21
Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.
22
Yakan bayyana zurfafa da ɓoyayyun abubuwa; ya san abin da yake cikin dare, haske kuwa yana zaune tare da shi.
23
Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”
24
Sai Daniyel ya tafi wurin Ariyok, wanda sarki ya sa yă kashe masu hikiman Babilon, ya kuma ce masa, “Kada ka kashe masu hikiman Babilon ka kai ni wurin sarki, ni kuma zan fassara masa mafarkinsa.”
25
Sai Ariyok ya kai Daniyel wurin sarki nan take ya ce masa, “Na gano wani mutum daga cikin kamammun kabilar Yahuda wanda zai faɗa wa sarki abin da mafarkin yake nufi.”
26
Sarki ya tambayi Daniyel (wanda ake kira Belteshazar), za ka iya faɗa mini mafarkin da na yi ka kuma fassara shi?
27
Daniyel ya amsa, “Babu wani mai hikima, ko mai sihiri, ko mai dabo ko mai duban da zai iya warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi,

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options