Ayyukan Manzanni 10:28-48
28
Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta.
29
Don haka sa’ad da aka aika in zo, na zo ba wata faɗa. To, ko zan san abin da ya sa ka aika in zo?”
30
Korneliyus ya amsa ya ce, “Kwana huɗu da suka wuce ina a gidana ina addu’a a wannan lokaci, wajen ƙarfe uku na yamma. Ba zato ba tsammani sai ga wani mutum cikin tufafi masu walƙiya ya tsaya a gabana
31
ya ce, ‘Korneliyus, Allah ya ji addu’arka, ya kuma tuna da kyautanka ga matalauta.
32
Ka aika zuwa Yoffa don a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman mai aikin fatu, wanda yake zama a bakin teku.’
33
Saboda haka na aika a zo da kai nan da nan, ya kuma yi kyau da ka zo. To ga mu duka a nan a gaban Allah don mu saurari dukan abin da Ubangiji ya umarce ka ka faɗa mana.”
34
Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai
35
amma yana karɓan mutane daga kowace al’ummar da take tsoronsa suke kuma aikata abin da yake daidai.
36
Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.
37
Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi,
38
yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
39
“Mu kuwa shaidu ne na dukan abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da kuma a Urushalima. Suka kashe shi ta wurin rataye shi a kan itace,
40
amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi.
41
Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu.
42
Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu.
43
Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
44
Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon.
45
Masu bin da suke da kaciya waɗanda suka zo tare da Bitrus suka yi mamaki cewa an ba da kyautar Ruhu Mai Tsarki har ma a kan Al’ummai.
46
Gama sun ji su suna magana da waɗansu harsuna suna kuma yabon Allah. Sai Bitrus ya ce,
47
“Wani zai iya hana a yi wa waɗannan mutane baftisma da ruwa? Sun karɓi Ruhu Mai Tsarki kamar yadda muka karɓa.”
48
Saboda haka ya ba da umarni a yi musu baftisma cikin sunan Yesu Kiristi. Sa’an nan suka roƙi Bitrus yă zauna da su na ’yan kwanaki.
Settings