2 Timoti 2:1-13
1
Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu.
2
Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.
3
Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.
4
Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.
5
Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki.
6
Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona.
7
Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.
8
Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata,
9
wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba.
10
Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.
11
Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi;
12
in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;
13
in ba mu da aminci, shi dai mai aminci ne, domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”
Settings