2 Sama’ila 13:30-39
30
Yayinda suke kan hanyarsu, sai labari ya kai kunnen Dawuda cewa, “Absalom ya kashe dukan ’ya’yan sarki maza; ko ɗayansu Absalom bai rage ba.”
31
Sai sarki ya tashi, ya yage tufafinsa, ya kuma kwanta a ƙasa; dukan bayinsa kuwa suka tsaya da rigunansu yagaggu.
32
Amma Yonadab, ɗan Shimeya ɗan’uwan Dawuda ya ce, “Kada ranka yă daɗe yă yi tunani cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza; Amnon ne kaɗai ya mutu. Wannan ce niyyar Absalom tun lokacin da Amnon ya yi wa Tamar ’yar’uwansa fyaɗe.
33
Kada mai girma sarki yă damu da jita-jitan nan cewa an kashe dukan ’ya’yan sarki maza. Amnon ne kaɗai ya mutu.”
34
Ana cikin haka, sai Absalom ya gudu. To, mutumin da yake tsaro a wannan lokaci ya ɗaga kai sai ya ga mutane da yawa a hanya, yamma da shi, suna gangarowa daga gefen tudu. Sai mai tsaron ya je ya gaya wa sarki cewa, “Na ga mutane ta wajen Horonayim, a gefen tudu.”
35
Yonadab ya ce wa Sarki, “Duba, ga ’ya’yan sarki maza sun zo; ya faru kamar dai yadda bawanka ya faɗa.”
36
Yana gama magana, sai ga ’ya’yan sarki maza suka shigo suna kuka da ƙarfi. Sarki ma da dukan bayinsa suka yi kuka mai zafi.
37
Absalom ya gudu ya tafi wurin Talmai ɗan Ammihud, sarkin Geshur. Amma Sarki Dawuda ya yi ta makokin ɗansa kowace rana.
38
Bayan Absalom ya gudu sai ya je wurin Geshur, ya zauna a can shekara uku.
39
Sai zuciyar sarki Dawuda ya komo kan Absalom, gama an yi masa ta’aziyya game da mutuwar Amnon.
Settings