Skip to content
2 Sama’ila 13:23-29

2 Sama’ila 13:23-29

23
Bayan shekaru biyu, sa’ad da masu askin tumakin Absalom suna Ba’al-Hazor, kusa da iyakar Efraim, sai ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza a can.
24
Sai Absalom ya je wurin sarki ya ce, “Bawanka ya sa masu askin tumaki sun zo. Ko sarki da fadawansa za su zo tare da ni?”
25
Sarki ya ce, “A’a ɗana, bai kamata dukanmu mu tafi ba; don kada nauyi yă yi maka yawa.” Absalom dai ya dāge, duk da haka sarki ya ƙi yă je, sai dai ya albarkace shi.
26
Sa’an nan Absalom ya ce, to, “In ba za ka ba, ina roƙonka bari Amnon ɗan’uwana yă zo tare da mu.” Sarki ya ce masa, “Don me zai tafi tare da kai?”
27
Amma Absalom ya nace don sarki yă yarda, saboda haka sarki ya bar Amnon da sauran ’ya’yan sarki maza su tafi tare da shi.
28
Absalom ya umarci mutanensa ya ce, “Ku saurara! Sa’ad da Amnon ya bugu sosai da giya na kuma ce muku, ‘Ku bugi Amnon,’ sai ku kashe shi. Kada ku ji tsoro. Ashe, ba ni ne na ba ku wannan umarni ba? Ku yi ƙarfin hali, ku kuma yi jaruntaka.”
29
Saboda haka mutanen Absalom suka yi wa Amnon abin da Absalom ya umarta. Sai dukan sauran ’ya’yan sarki maza suka hau dawakansu suka gudu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options