Skip to content
2 Sarakuna 22:1-14

2 Sarakuna 22:1-14

1
Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat.
2
Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.
3
A shekara ta goma sha takwas ta mulkinsa, Sarki Yosiya ya aiki Shafan ɗan Azaliya, ɗan Meshullam, magatakarda, zuwa haikalin Ubangiji. Ya ce,
4
“Ka haura zuwa wurin Hilkiya babban firist ka sa yă shirya kuɗin da aka kawo a haikalin Ubangiji, wanda masu tsaron ƙofa suka tara daga mutane.
5
Ka sa su danƙa su a hannun waɗanda aka zaɓa don biyan ma’aikatan da suka yi gyara a haikalin Ubangiji,
6
wato, kafintoci, da magina, da masu tsara gini. Ka kuma sa su sayi katakai da sassaƙaƙƙun duwatsu don a gyara haikalin.
7
Amma ba sa bukata su ba da bayanin kuɗin da aka danƙa musu domin suna aikinsu da aminci.”
8
Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta.
9
Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”
10
Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki.
11
Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa.
12
Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce,
13
“Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”
14
Sai Hilkiya firist, da Ahikam, Akbor, da Shafan, da kuma Asahiya suka je don su yi magana da annabiya Hulda, matan Shallum ɗan Tikba, ɗan Harhas, mai ajiyar tufafi. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options