Skip to content
2 Sarakuna 21:19-26

2 Sarakuna 21:19-26

19
Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.
20
Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi.
21
Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu.
22
Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.
23
Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.
24
Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.
25
Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.
26
Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options